Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Hizbullah ta Lebanon: A yau muna gab da samun gagarumar nasara mai tarihi. Zuwa ga mutane mafi daraja... ga al'ummar juriya da haƙuri dagewa da sadaukarwa ga mutanen Kudu masu juriya, abubuwan alfahari da ɗaukaka...
A yau mun tsaya a kan gagarumar nasara mai girma ta tarihi; Nasarar da za a sameta ta hanyar sadaukarwar mujahidai, da jinin shahidai da hakurin ku mara misaltuwa...da yankunan da aka kaiwa hari a Dahiyat Junub da kuyi hakuri haar zuwa sanardar da takamaiman tsagaita wuta a hukunce; Domin wannan maƙiyi yana da yaudara da muguwar nufi, wanda ke ƙoƙarin tserewa a yanayin shan kaye, na iya ɗaukar matakan don ƙirƙirar fage na karya kuma ya yi kamar ya sami nasarar da ba zai iya cimmawa a fagen fama ba. Za ku koma ƙauyuka da gidajenku nan ba da jimawa ba cikin lfahari da daukaka, masu kauna da samun nasara, kamar yadda kuka kasance koyaushe.
Your Comment